Fxtrade
Would you like to react to this message? Create an account in a few clicks or log in to continue.

Go down
avatar
Admin
Posts : 14
Join date : 2022-01-02
View user profilehttps://fxtrade.africamotion.net

Wikifx:Saye da sayarda jerin kudade guda biyu. Empty Wikifx:Saye da sayarda jerin kudade guda biyu.

Fri Jan 07, 2022 5:48 am
Kasuwar canji shi ne siyan kudi daya da kuma siyar da wani kudin a lokaci guda.

 Ana cinikayyar kudade ta hanyar “dillalan canji” ko makamantan hakan, kuma ana cinikayyarsu ne da biyu-biyu. Ana saka farashin Kudaden ne ta hanyar danganta su da wani kudin.

 Misali, euro da U.S.dollar (EUR/USD) ko kuma fam din Birtaniya da Yen din Japan (GBP/JPY)

 Idan kayi cinikayya a kasuwar canji, kana siya ko siyarda kudade ne a biyu-biyu.

saye.png
 Ka kaddara cewa kowanne hadin kudade biyu suna fafatawa a tsakaninsu kowanne yanason ya rinjayi dan uwansa

 Farashin canji shi ne dangantakar farashin kudade guda biyu na kasashe biyu daban daban.

 Farashin canji yana hawa yana sauka, wanda hakan ya ta’allaka ne da kudin da yafi karfi a wannan lokacin.

 An kasa jerin kudaden biyu izuwa kashi uku:

 Akwai “majors”

 Akwai “crosses”

 Akwai “exotics”

 Su manyan kashi (majors) akoda yaushe akwai U.S dollar a tare dasu.

 Cross-currency sukuma wannan kashin basa tareda da U.S. dollar. Kashin Crosses din dasuke tare da manyan kudade ana kiransu da suna “minors”.

 Exotic currency, sukuma wannan kashin sun hada da daya daga cikin manyan kudade da kuma daya daga cikin kudaden kasuwa mai tasowa.

 Manyan Jerin kudade biyu

saye1.png
 Wadannan kudade masu biyu da aka jero a kasa ana daukansu a matsayin manyan kudade (majors).

 A wannan jerin gaba dayansu suna dauke da U.S. dollar a bangare daya, kuma sune akafi kasuwancinsu.

 Duk da cewa akwai manyan kudade guda takwas, akwai jerin kudade masu biyu guda bakwai kacal.

 Farashi yafi motsawa a tareda da majors akan crosses dakuma exotics, wannan shi yake bada dama mai yawa ta kasuwanci.

saye2.png
 Manyan kudade wato majors su akafi “yawan cinikayyarsu” a duniya.

 Yawan cinikayya ana amfani dashi ne wajen kwatanta yawan kasuwanci a kasuwar kudi.

 A kasuwar canji, yana nuni ga yawan yan kasuwar da suke siye da sayar da kayyadadden jerin kudade biyu dakuma adadin da ake cinikayya dasu.

 Yawan saye da sayar da abu shi yake kara yawan cinikayyarsa a kasuwa.

 Misali, mutane mafiya yawa suna cinikayyar jerin kudaden EUR/USD a ma’auni mai girma fiyeda jerin kudaden AUD/USD.

 Wannan yana nufin EUR/USD anfi yawan cinikayyarsa akan AUD/USD

 Manyan kudaden ketare (jerin biyu) ko kuma

 Kananan Kudade (Jerin biyu)

 Kudade masu jerin biyu da suke dauke da manyan kudade a tare dasu banda U.S dollar su ake kira kudaden ketare masu biyu biyu ko cikin sauki ace ‘kudaden Ketare”.

 Manyan kudaden ketare ana kiransu da “Kananan Kudi”.

 Duk da cewa ba’a kasuwancinsu kamar manyan kudade, suma kudaden ketare ana cinikayyarsu kuma suma suna bada damar kasuwanci mai yawa.

 Karka rikice tsakanin kananan jerin kudade masu biyu dakuma manyan jerin kudade masu biyu guda bakwai, domin kuwa gaba dayansu suna dauke da U.S.dollar akan daya daga cikin ragowar kudade guda shida wadanda akafi yawan cinikayyarsu a duniya.

 Kudaden ketaren da akafi amfani dasu an samosu ne daga manyan kudade banda U.S. dollar acikinsu: EUR, JPY, GBP.

 Kudaden ketare na Euro

saye3.png
 Kudaden ketare na Yen

saye4.png
 Kudaden ketare na Pound

saye4.png
 Ragowar Kudaden ketare

saye6.png
 Bakin jerin kudade biyu

saye7.png
 A’a bakin jerin kudade biyu bawai yan rawa bane wanda suke yan biyu.

 Bakin jerin kudade biyu kudade ne daga kasashe masu tasowa ko kasuwanni masu habaka.

 Bakin jerin kudade biyu sun hadane da daya daga cikin manyan kudade tareda daya daga cikin tattalin arziki mai habaka kamar na kasar Brazil, Mexico, Chile, Turkey, or Hungary.

 A takaice, bakin jerin kudade biyu yana dauke da daya daga cikin manyan kudade da kuma bakon kudi guda daya a tare dashi.

 Wannan taswirar ta kasa tana dauke da misalai na bakin jerin kudade biyu.

 Shin kanada sha’awar yin yar canke akan me alamomin ragowar kudaden suke nufi?

 Ya danganta da dillalan kasuwar canjin, zaka iya ganin wadannan bakin jerin kudaden biyu masu zuwa, saboda haka yana dakyau kasan me suke nufi.

 Kasaka aranka cewa wannan jerin kudaden masu biyu basu kai manyan kudade dana ketare ba wajen karbuwa da cinikayya saboda haka kudin hadahadarsu yanada tsada.

saye8.png
 Ba abun mamaki bane ba kaga shimfidodi da suka ninka na EUR/USD ko USD/JPY sau biyu ko sau uku.

 Saboda karancin cinikayyar bakin jerin kudade biyu sai yasaka suka kasance canjin tattalin arziki da siyasar bangarori yana saurin shafar su.

 Misali, abun kunya a siyasa ko sakamakon zabe na bazata suna iya sakawa farashin canjin bakin jerin kudade biyu yayi mummunar canjawa.

 Saboda haka idan kanaso kayi cinikayyar bakin jerin kudade biyu, karka manta kasaka wannan abun a ranka.

 Ga wadanda bakin jerin kudade biyu suke birgesu, ga cikakken jerinsu nan.

saye9.png
saye10.png
saye11.png
 Shin kasani kuwa? Akwai yardaddun kudade guda 180 a duniya, wanda majalisar dinkin duniya ta yarda dasu. Adadinsu yanada yawa idan akace za’a jera su a kudade biyu-biyu. Sai dai kash, ba gaba dayansu ake iya karantawa ba. Dillalan kasuwancin kudi suna bada guda 70 daga cikinsu ne kawai a matsayin wadanda za’a iya kasauwanci dasu.

 Bayan wadannan kashi uku na jerin kudade biyu, akwai wasu kashin na kudaden da aka watsa su cikin duniya wanda ya kamata kasan dasu.

 Kudaden G10

 Kudaden G10 kudade ne guda goma wanda akafi kasuwanci dasu a duniya, wanda kuma sune kudade guda goma wanda akafi cinikayya dasu a duniya.

 Yan kasuwa suna siye da sayar dasu akai akai a budaddiyar kasuwa da dan karamin tasiri akan farashin canjin su na duniya.

saye13.png
 Scandies

 Scandinavia wani bangare ne a arewacin Europe mai tarin tarihi, al’adu da yarirrika.

 Kalmar “Scandinavia” a gargajiyance ta hada da masauratu guda uku na kasar Denmark, Norway, dakuma Sweden.

 Gaba daya kudinsu shi ake kira da “Scandies”.

 A zamanin da, Denmark da Sweden sun kirkiri hukuma mai suna Scandinavian Monetary Union doimin su hade kudadensu yazama daidai da darajar gwal. Daga baya Norway suma suka mara musu baya.

 Wannan yana nufin cewa kasashen suna amfani da kudi daya mai daraja daya saidai kowacce kasa ita take buga nata kudin.

 Amma bayan yakin duniya na farko, daidaito da darajar gwal ya watse hukumar tasu ta Scandinavian Monetary Union ta tarwatse. Wannan kasashen sunci gaba da amfani da kudadensu duk da darajarsu ta bambanta.

 Haka al’amarin yacigaba da wakana.

 Idan ka kula da sunayen kudadensu, duk suna kama da juna, Kalmar “krone” ko “krona” tana nufin “crown” wato kambun sarauta. Sannan bambancin rubutun yana nuni ga bambancin yaruka na arewa da Germany.

 Kudaden kambun sarauta. Sunan yayi dadi ko?

 Bansan dai a gurinka ba, amma cewa “Hadani da kambun sarauta” yafi armashi akan “Hadani da dollar”

saye14.png
 SEK da kuma NOK suma sunada sunayen wasa masu armashi, “Stockie” da kuma “Nockie”.

 Saboda haka idan aka hada U.S.dollar, USD/SEK ana karantashi kamar haka “dollar stockie” sannan USD/NOK ana karantashi kamar haka “dollar nockie”.

 Kudaden CEE

 “CEE” tana nufin central da kuma Eastern Europe, ma’ana Europe ta tsakiya da Europe ta gabas.

 Europe ta tsakiya da Europe ta gabas yana nufin kasashen da suke Europe ta tsakiy, Baltics, Europe ta gabas da Europe ta kudu (Balkans), sau da yawa ana nufin tsofaffin garuruwan kwaminisanci daga gabas da Bloc (Warsaw Pact) a Europe.

 Kasashen Europe ta tsakiya da Europe ta gabas (CEECs) kalma ce ta OECD wadda take nufin kasashen da suka hada da Albania, Bulgaria, Croatia, the Czech Republic, Hungary, Poland, Romania, the Slovak Republic, Slovenia, dakuma garuruwan Baltic guda uku: Estonia, Latvia, ddakuma Lthuania.

 A bangaren kasuwar canji, akwai muhimman kudaden CEE guda hudu da yakamta kasan dasu.

saye15.png
 BRIICS

 BRIICS takaitaccen suna ne da yake da alaka da taron kasashe guda shida masu masu tasowa a tattalin arziki: Brazil, Russia, India, Indonesia, China, South Africa.

 Ainahi guda hudun farko su aka tattare a matsayin “BRIC” (ko “the BRICs”).

 Kalmar BRICs an samota ne a wajen Goldman Sachs domin a samar da sunayen manyan tattalin arziki masu tasowa.

 BRIICS an kikiro tane ne daga wajen OECD, sanda ta kara Indonesia da South Africa.

saye16.png
 Bayani atakaice

 Anyi bayani mai yawan gaske akan kudade, amma yanzu ka kara ilimin ka na kasuwar canjin kudi.

 Bara muyi bayani a takaice akan abunda aka koya a matsayin jerin tambayoyi.

 Mene ne jerin kudade biyu a kasuwar canji?

 Jerin kudade biyu shi ne jera kudade guda biyu ta yadda darajar daya daga cikinsusu zai zama yanada alaka dana dayan. Misali, GBP/USD shine darajar kudin Birtaniya wanda yakeda alaka da darajar kudin Amurca.

 Su wadanne ne Manyan jerin kudade biyu?

 Manyan jerin kudade biyu (majors) su ne wanda suke dauke da U.S. dollar kuma a koda yaushe acikin cinikayyarsu ake. Guda bakwai ne gaba dayansu: EUR/USD, GBP/USD, USD/CAD, USD/CHF, AUD/USD, and NZD/USD.

 Su wadanne ne kudaden ketare?

 Kudaden ketare (crosses) su ne akafi cinikayyarsu wanda basa dauke da U.S. dollar sun hada da EUR/GBP, EUR/CAD, GBP/JPY, EUR/CHF, EUR/JPY etc.

 Jerin kudade biyu guda nawane?

 Akwai DARURUWAN jerin kudade biyu a duniya, amma bagaba dayansu ake iya cinikayya dasu ba a kasuwar canjin kudi. Majalisar dinkin duniya ta amince da kudade guda 180. Idan akace za’a jera kowanne kudi da wani kudin, abun zaiyi yawa.


https://minnews.wikifx.com/What-is-Forex/2-What-Is-Traded-In-Forex.html
Back to top
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum