Fxtrade
Would you like to react to this message? Create an account in a few clicks or log in to continue.

Go down
avatar
Admin
Posts : 14
Join date : 2022-01-02
View user profilehttps://fxtrade.africamotion.net

Wikifx:Me ake ciniki a Forex? Empty Wikifx:Me ake ciniki a Forex?

Thu Jan 06, 2022 6:28 am
Me ake ciniki a Forex?

 Amsa mafi sauki ita ce KUDI. Ma’ana kudaden kasashe.

 Saboda ba wani abu ake siya a zahiri ba, kasuwancin canji yanada yar rikitarwa, saboda haka zamuyi amfani da misali maisauki dazai taimaka wajen bayaninsa.

 Ka kaddara cewa siyan kudi kamar siyan hannun jari ne a wata Kasa, kamar siyan hannun jari ne a masana’anta.

 Farashin kudi mafi yawanci yana nuni ga ra’ayin kasuwa akan ingancin tattalin arzikin kasuwar na yanzu da kuma na nan gaba.

 A kasuwar canji, idan kasayi misali, kudin Japan (yen), to bakomai kakeyi ba face siyan hannun jari a tattalin arzikin Japan.

mkr.jpg
 Kayi yaqinin cewa tattalin arzkin Japan yana tafiya yadda ya kamata kuma za’a samu cigaba nan gaba.

 Idan ka siyar da wadannan “hannayen jarin” a kasuwa, ana saran zaka ci riba.

 A gaba daya, farashin canjin kudi zuwa wasu kudaden yana nuni da yanayin tattalin arzikin wannan kasar akan tattalin arzikin wayancen kasashen.

 Daga lokacin daka gama makarantar Pipsology, zaka kagu kaga kafara aiki da kudaden kasashe daban daban.

 Manyan Kudade

 Kamar yadda akwai kudade da yawa da zaka iya kasuwancin su, a matsayinka na sabon dan kasuwar canji, tana yiwuwa kafara kasuwancin da manyan “kudade”.

mkr.jpg
 Su ake kira “manyan Kudade” saboda sune kudaden da akafi kasuwancin canji dasu sannan kuma wasu daga cikinsu suna nuni da mafi girman tattalin arziki na duniya.

 Yan kasuwar canji sunyi sabani akan kudaden da suke kira da Manyan Kudade.

 Wanda suke yan ka’ida daga cikinsu, masu bin dokoki kamar yara sun dauki USD, EUR, JPY, GBP, dakuma CHF a matsayin manyan kudade.

 Sannan suka kira AUD, NZD, dakuma CAD da sunan “kudaden Haja”.

 A gurin mu mu yan tawaye, sannan dan mu saukaka abun, kawai muna kiran gaba daya kudade takwas din da sunan “manyan kudade”.

 Akasa, mun jerosu tareda alamominsu, Kasashen da ake amfani dasu, sunayen kudaden dakuma sunayen wasan su masu armashi.

mkr.jpg
mkr.jpg
 Kudade sunada alamomi na “harafai uku”, harafai biyun farko suna nuni ne izuwa ga sunan kasar da ake amfani dasu, shikuma harafi na karshe yana nuni izuwa ga kudin kasar da ake amfani dasu, mafi yawanci yana nuni ga harafin farko na kudin kasar.

 Wadannan harafai guda uku su ake kirada ISO 4217 Currency codes.

 A shekarar 1973, hukumar shiryawa da daidaita kudi ta duniya (ISO) sun samar da harafai guda uku a matsayin alamomin kudaden da muke amfani dasu yanzu.

mkr.jpg
 Mudauki NZD a misali……

 NZ tana nufin New Zealand, ita kuma D tana nufin dollar.

 Abu mai sauki, ko?

 Kudaden da suke cikin wannan taswirar ta sama su ake kira da “Manyan Kudade” saboda sune kudaden da akafi kasuwanci dasu.

 Shin kasani kuwa? Kudin Britaniya (pounds) shi ne kudin da yafi kowanne dadewa a duniya wanda har yanzu ake amfani dashi, anfara anfani dashi tun daga karni na takwas (8th century). Sabon kudi a duniya shi ne kudin kasar Sudan ta kudu (South Sudan Pound), an tabbatar dashi a hukumance ranar 18 ga watan yuli, 2011.

 Zamuso kusan cewa “buck” bashi kadaine sunan wasa na USD ba.

 Akwai wasu kamar su: greenbacks, bones, benjis, benjamins, cheddar, paper, loot, cheese, bread, moolah, dead president and cash money.

 Saboda haka idan kanaso kace “Yanzu zan tafi aiki”

 Zaka iya cewa, “Yo, I gotto bounce! Gotto make benjis son!”

 Mudan yi Raha: A garin Peru, sunan wasan U.S. dollar shi ne Coco, wanda sunan dabba ne Jorge (George a yaren Spanish), wanda yana nuni ne da taswirar George Washinton ajikin dalla daya ($1 note)

mkr.jpg
Suna kirana da Coco yo!
https://minnews.wikifx.com/What-is-Forex/2-What-Is-Traded-In-Forex.html
Back to top
Permissions in this forum:
You cannot reply to topics in this forum